Zargin rufe bakin 'yan fafutika a Najeriya
September 28, 2016Talla
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta bayyana cewa Najeriya na kokari da barazana ta rufe baki da ma yin barazana ga 'yan jarida da masu zanga-zanga.
A cewar kungiyar wacce ke da ofishinta a birnin London cikin zanga-zangar da ta bayyana a baya-bayan nan akwai hana masu fafutika daga kungiyar nan mai kokari na ganin ansako 'yan matan Chibok sama da 200 da ke hannun Boko Haram, da hana 'yan Shi'a zanga-zangar a sako malaminsu bayan tsawon lokaci ya na hannun mahukunta da masu fafutikar samun 'yancin yankin Biafra a Kudu maso Gabashin na Najeriya.