Zargin ci zarafin yara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
April 1, 2016Talla
MDD ta soma gudanar da wani sabon bincike a kan cin zarafin yara 'yan mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wanda ake zargin sojojin rundunar na Ƙasar Faransa watau Sangari da laifin aikatawa.A cikin wata sanarwa da wata ƙungiya mai zaman kanta da ke a birnin New York da ake kira da sunan Aids Free World ta bayyana,ta ce 'yan mata aƙalla guda 98 suka ba da shedun cewar tsakanin shekara ta 2013 zuwa wannan shekara.
Cewar sojojin rundunar na kiyaye zaman lafiya na MINUSCA na ƙasashen Gabon da Kwango da Burundi sun ci zarafinsu. Kana kuma suka ce daga cikin sojojin har'da wani na Ƙasar Faransa wanda ya riƙa tilasta wa 'yan mata yin jimai da karnuka