Zanga-zangar yan sanda a zirin Gaza | Labarai | DW | 01.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar yan sanda a zirin Gaza

Dubbunan yan sanda, a Palestinu sun shirya zanga zanga sahiyar yau, a zirin Gaza.

Jami´an tsaron, na bukatar gwamnatin Hamas ta biya su albashin wattani da dama, ta kuma kauttata masu rayuwa.

Rahotani na nuni da cewar,tun hawan gwamnatin Hamas kan karagar mulki, a watan Maris da ya wuce, wannan itace zanga-zanga mafi girma, da a ka shirya a ƙasar.

Kazalika, masu zanga zangar ,sun yi Alah wadai, da aniyar Praminista Ismael Hanniyeh, ta biyan su albasjhi da guntu guntu.

Yan sandar, sun yi kaca kaca da ginin majalisar dokoki ta zirin Gaza.

Yau wattani 3 kenan, da su wuce, gwamnati ta kasa biyan albashin ma´aikata, kimanin dubu 165, a dalili da matakin tsuke bakin aljihu, da Amurika, da kuma ƙungiyar gamaya turai, su ka ɗauka, a kan da sabuwar gwamnatin.

Su na masu bukatar Hamas ta yi watsi da manufofin ta , na haramta ƙasar Isra´ila, da kuma kwance ɗamara yaƙi da dakarun ta.