Zanga zangar yan daliban Afrika a rasha | Labarai | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar yan daliban Afrika a rasha

Daruruwan dalibai yan Afrika suka yi wata zanga zanga a yau talata game da kashe wani dalibi dan afrika da akayi a birnin St Petersburg na kasar Rasha.

A ranar asabar ne wasu da yan bindiga suka kashe wani dalibi dan kasar Kamaru,wani kuma ya samu rauni,kisan da daliban suka ce yana da alaka da bambancin launin fata.

Yan tsirarun kugiyoyi masu goyon bayan yan Nazi wadanda har yanzu da sauran burbushinsu,suna kai hare hare akan yan Afrika da kuma Asiyawa a Rasha.

A birnin St Petersburg kadai,yan Afrika da Asiya akalla 10 ne aka kashe cikin hare hare irin wannan cikin shekaru 2 da suka shige .

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sunyi gargadin cewa yan siyasa suna kara hura wutar tsana na launin fata.

A farkon wannan wata ne,aka dakatar da jamiyar Rodina shiga zabe a birnin Masko,bayan jamiyar cikin takardun kanfe dinta tayi kira ga mazauna birnin da su kawadda dauda daga birnin tana mai nuna hotunan bakar fata da Asiyawa .