1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar yan assulin Habasha mazauna kasar Jamus

Yahouza SadissouNovember 6, 2005

Yan assulin Habasha dake zaune a Jamus sun shirya zanga zangar nuna kin jinnin Praminista Meles Zenawi

https://p.dw.com/p/Bu4Q
Hoto: AP

Demokaradiya muke bukata , ba mu amince ba, da mulkin danniya da kama karya, mu na Allah waddai, da mulkin Meles Zenawi, kadan kenan daga kalamomin da daruruwan yan assulin Habasha dake zaune a nan kasar Jamus, su ka yi ta rerawa, a wata zanga zangar da su ka shirya, domin nuna kin jinin Praministan Ethiopia Meles Zenawi.

Yan Habasha mazamna Jamus, sun kiri wannan zanga zanga, a yayin da Praminista Zelawi ke halartar taro , a nan Jamus, bisa gayyatar shugaban kasa Host Kohler, tare wasu sauran shuwagabani na Afrika, da su ka hada da Olesegun Obasanjo na Tarayya Nigeria, da Tabon Mbeki, na Afrika ta kudu, da kuma Alfa Umar Konare, shugaban kungiyar tarayya Afrika.

Sun shirya zanga zangar, a harabar tsohuwar fadar magajin garin birnin Bonn.

A hira da na yi da Dr Azafa, jagoran masu zanga zangar, ya sanar da ni cewa, babban makasudin shirya ta, shine na nuna bacin rai, ga kissan gillar da ke wakana a kasar Ethiopia, inda a tsukin yan kwanaki 5 da su ka gabata, jami´an tsaro su ka hallaka mutane kimanin 50, da kuma capke a kalla mutane 2000 na jam´iyun adawa.

Ya ce Praministan Ethiopia, ya shinfida mulki irin na fir´aunanci tare da nuna wariya, kabilanci ,da kama karya.

Kalika a cewar sa,yan Habasha masu kishin Demokradiya, sun hitto kwan su da kwalkawta,don nuna kin aminewa da magudin da ka tabka, ta hanyar aringizon kuri´u, a lokacin bayyana sakamakon zaben yan majalisun dokoki na watan mayu da ya gabata, zaben da ya baiwa Meles Zemawi, damar zarcewa bisa karagar mulkin kasa.

A daya hannun wannan zanga zanga na da manufar goyan baya, ga dubunan mutanen da Jami´an tsaro ke tsare da su ,a yanzu haka, a gidajen kurkuku da kuma nuna takaici ga kissan gillar da ya abku a kasar , sannan wannan wata dama ce, ta shaidawa dunia , zahiri halin ukuba da a ke ciki a kasar Habasha inji Dr Azafi.

Jagoran masu zanga zangar na birnin Bonn,ya bayyana bacin rai, a kan yadda hukumomin Jamus da na wasu sauran kasashen turai, ke daurewa karya gindi, a game da hadin kai, da su ke baiwa Meles Zenawi.

A wani abu da ke iya zama cimma biyan biyan bukata take yanke, kiran na yan kasar Habasha, ga alamu ya shiga kunnuwa da ta kamata.

A yammacin jiya, jikadodin kungiyar Gamayya Turai, da Amurika, da ke birnin Addis Abbaba, sun hido sanarwar hadin gwaiwa, inda su ka bukaci hukumomin kasar sun yi belin daukacin mutanen da su ka kama a cikin zanga zangar bayan bayan.

Jikadan kasar Britania Bob Dewar, da ya karanta sanarwar ga manema labarai ,ya nuna bacin ran kasashen dunia, a game da wulakancin da jami´an tsaron Habasha su ka yiwa jama´a.

Ya yi kira ga gwamnati, da ta yi belin dukan wanda su ka tsare su kuma dakatar da bincike na babu gaira, babu dalili da su ci gaba da yi ga mutanen da su ba su san hawa ba, balle sauka.

A halin da ake ciki, baki daya shuwagabanin jam´iyar adawa ta CUDP, na tasare gidan kurkuku, abinda ya sabawa demokaradiya da ka´idojin ta, inji Ambassada Bob Dewar.