Zanga-zangar ′yan adawa a Kwango duk da haramcin kotu | Labarai | DW | 25.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar 'yan adawa a Kwango duk da haramcin kotu

'Yan adawa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango sun lashi takobin gudanar da zanga-zanga duk da haramcin yin haka.

Kungiyar 'yan adawa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da ta fusata sakamakon wani hukuncin kotu da ya yarda Shugaba Joseph Kabila ya cigaba da zama kan karagar mulki bayan cikan wa'adin mulkinsa, ta lashi takobin gudanar da zanga-zangar kasa baki daya don bijire wa haramcin yin hakan a wasu sassan kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar The Citizens Front ta ce yin wata zanga-zanga da ba ta saba wa doka ba, wani 'yanci ne da kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. Hukumomi dai a lardin Kivu ta Arewa mai fama da rikici da ke gabashin Kwango da kuma a Lubumbashi birnin na biyu mafi girma a kasar da ke kudu, sun haramta gudanar da zanga-zangar. To sai dai kungiyar The Citizens Front ta ce za ta yi jerin gwano a fadin kasar a wannan Alhamis din don adawa da hukuncin kotun tsarin mulki da ta ce Kabila ka iya cigaba da mulki a matsayin shugaban riko bayan cikar wa'adin shugabancinsa a watan Disamba.