1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

zanga zangar Sunni da Shia a Iraqi

Magoya bayan yan sunni fiye da 10,000 da yan shia masu sassaucin raayi ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Bagadaza,suna masu kira da a kafa gwamnatin hadaka a Iraqi.

Masu zanga zangar suna masu cewa babu ruwansu da sunni ko shia abinda suke bukata shine hadin kan kasa.

Daya daga cikin masu zanga zangar yace sunyi Allah wadai da sakamakon zaben yana mai fadin cewa ina kuriunsu suka tafi.

Ana kuma ci gaba da kai hare hare akan jamian tsaro,wasu yan sanda 6 da wasu farar hula 2 sun rasa rayukansu a yau din,a kudancin Bagadaza

Rundunar sojin Amurka a Iraqi tace wasu matuka jirginta 2 sun rasa rayukansu a lokacinda jirgi mai saukar angulu ya fadi a daren jiya.

Wasu masu aikin hanya kuma a Karbala sun gano gawarwakin mutane da dama da yan sanda suka ce mai yiwu ne mutanen da Saddam ya kashe ne lokacinda yan shia suka tashi yiwa gwamnatinsa bore a 1991.