Zanga zangar nuna kin jinnin Georges Bush a Amurika | Labarai | DW | 03.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar nuna kin jinnin Georges Bush a Amurika

Dubun dubatar mutane ne, a biranen New York Los Angeles, Seattle, San Fransisco, da Chicago su ka shirya zanga zangar nuna kin jinnin Shugaban Georges Bush na Amurika, mussamman a game da yadda ya nuna halayen ina ruwa na ga mutanen da billa´in Katrina ya rutsa da su, a kwanakin baya, da kuma siyasar gwamnatin sa, a kasar Iraki.

Kungiyoyi daban daban sun girka wata hadadiyar kungiya da su ka sawa suna The World can´t wait, wato dunia ba za ta jira ba, domin kalubalantar shugaba Bush, ta hanyar cilas masa yayi murabus.

Daya daga wanda su ka jagoracin zanga zangar ta sannar maneman labarai cewa,Amurikawa sun gaji da sa ido, su na kallon Georges Bush ya na zubda masu mutunci, a dunia.

Cemma a ranar jiya tsofan shugaban kasar Amurika Jimmy Karter ya zargi Bush da bata suna Amurikawa da kuma wargaza tubbalen tushe, da ke tallabe da Amurika.

A daidai ranar wannan zanga zanga, Karin sojojin Amurika 4 sun mutu a kasar Iraki, a yammacin jiya.

A halin yanzu a jimilce Amurika ta rasa sojoji 2.028 a kasar Iraki.