1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar nuna adawa da ƙuri´a raba gardama a Venezuela

Dubun dubatan ´yan ƙasar Venezuela ƙarƙashin jagorancin ɗalibai sun yi zanga-zangar nuna adawa da wata ƙuri´ar raba gardama da zata bawa shugaba Hugo Chavez damar ci-gaba da tsayawa takara har muddin rayuwarsa. Masu zanga-zangar sun yi maci a tsakiyar babban birnin Venezuela, Caracas suna masu nuna adawa da yiwa tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima don bawa shugaba Chavez ikon hana yada labaru a lokacin dokar ta baci. Ƙuri´ar raba gardamar da za´a kaɗa a ranar lahadi ta taimaka wajen dinke baraka tsakanin ´yan adawar kasar wadanda ke fargabar cewa mulkin demokuraɗiyya zai kau a kasar ta Venezuela. Binciken jin ra´ayin jama´a ya yi nuni da cewa ko wane ɓangare na iya yin nasara.