Zanga-zangar nuna ƙin jinin Amurika a Khartum | Labarai | DW | 27.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar nuna ƙin jinin Amurika a Khartum

Ɗaruruwan masu zanga ne, a birnin Khartum na ƙasar Sudan, su ka tarbi Jendayi Frazer, mataimakiyar sakatare mai kulla da harakokin da su ka shafi Afrika, a fadar gwamnatin Amurika.

Jendayi Frazer, ta ziyarci Sudan ɗauke da wasiƙar shugaba Georges Bush , zuwa ga takwaran sa, Omar El-Beshir, domin roƙon sa, ya amince Majalisar Dinkin Dunia, ta tura dakaru a yankin Darfur, da ke fama da rikici.

Ranar alhamis da ta wuce, komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya kaɗa ƙuri´ar amincewa da tura rundunar shiga tsakani, a yankin Darfur, hukumomin Khartum, sun bayyana,yin wasti da wannan ƙuduri.

Shugaban El Beshir, ya gabatar da tsarin sa, na aika dakaru fiye da dubu 10 ,a yankin, amma Amurika, da sauran ƙasashen komitin sulhu, sun bayyana adawa da tsarin.

A wani ɓangaren kuma jiya ne kotun birnin El-Fashir a arewancin Sudan ta gurfanar da wakilin National Geographic, wata jaridar ƙasar Amurika.

Kotu ta tuhumi Paul Salopeck da lefin leƙen assirin ƙasa a lokacin da ya ziyarci yankin Darfur, ba tare da Visa ba, kokuma izinin gwamnatin Khartum.