1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar matasa a ƙasar France

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4v

Matasan ƙasar France,na ci gaba da zanga zanga, domin nuna adawa, da sabuwar dokar da Praminista Domonique De Villepin, ya ɗauka, mai suna CPE wato Contrat Premiere Ambauche.

A cikin wannan sabuwar doka, da a halin yanzu a ke ta kai ruwa rana a kan ta, a France, gwamnati ta tanadi cewar, nan gaba, kampani na gwamnati, ko mai zaman kan sa,na da izinin sallamar sabin ma´aikatan da zai ɗauka, muddun buƙatar hakan ta taso, ba tare da ya basu wata hujja ba.

Saidai gwamnati ta yi alkawarin bada tallafi ga wannan ma´aikata da a ka salama.

Dalilin daukar wannan mataki, inji Praministan, shine na ƙara faɗaɗa samar da wuraren aiki, ga matasa, da a halin yanzu, da dama daga cikin su, ke fama da zaman kashe wando.

Kungiyoyin ƙwadago, yan makaranta, da jami´iyun adawa, sun bayyana shiga ƙafar wando guda da gwamnati ,har sai loakcinda ta lashe amen ta.

A jawabin da yayi yau, gaban yan majalisar dokoki Dominique de Villepin ya jaddada zartas da wannan doka, ya kuma suka da kakkaussar harshe ga madugun yan adawar France, Francois Hollande da ke ƙara rura wutar rikicin.