Zanga-zangar mata a Kwango
October 18, 2010Duban mata sun gudanar da marchi a Bukavu yankin da ke a gabacin Jamhuriyar demokaradiyar kwango,domin nuna damuwarsu, da cin zarafin da mata ke fuskanta a yankin daga Ƙungiyoyin mayaƙa daban daban.
Jerin gwanon wanda ƙungiyoyin ne ´yan fafutuka su ka yi kiran sa ya samu halarta wakilai 1700 daga yankin kudanci da kuma gabacin Kivu,a ciki har da matar shugaba Joseph Kabila tare kuma da wakilci wasu mata 200 daga ƙasashen duniya 43.
Wani rahoton da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana ya nuna cewa mata sama da dubu goma sha biyar ne aka yiwa fyaɗe a shekara ta 2009 a gabacin Kwango, wanda kuma ake zargin dakarun gwamnatin da na ´yan tawaye da aikata laifufukan.
Mawallafi: Abdurahaman Hassane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi