Zanga zangar mahukuntan Pakistan | Labarai | DW | 14.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar mahukuntan Pakistan

Mahukuntan kasar Pakistan ,sun shirya gudanar da zanga zanga a yau talata zuwa ofisoshin jakadancin kasashen ketare a babban birnin kasar,domin nuna rashin jin dadinsu game da zanen batunci da akyiwa addinin Islama.

Wani dan majalisar kasar ya baiyana cewa,yan majalisa daga dukkan jamiyu siyasa na kasar ciki har da jamiyar dake mulki zasuyi maci daga majalisar su ratsa ta kan babban titin babban birnin kasar zuwa yankin dake dauke da ofisoshin jakadancin kasashen waje.

Dan majalisa Nayyar Bokhara yace,masu zanga zangar zasu mika takaradar nuna bacin ransu ga ofisoshin jakadancin kasashen Denmark da Norway.

Yace ya kamata kasashen su nemi gafara daga alummar musulmi,su kuma tabbatar musu da cewa ba zaa a kara buga irin wadannan zane zane ba nan gaba.