1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga Zangar Magoya Bayan Henri Konan Bedie

Magoya bayan tsofon shugaban Kasar Abiru Kwas sun ce a kwai kura kurai cikin sakamakon zaben da aka gudanar

default

Magoya bayan Henri konan Bedie

A ƙasar Cote d'Ivoire yanzu haka ana kan hanyar kaiwa ga zagaye na biyu na zaɓen shugaban kasa bayan da hukumar zaɓen ta kammala ƙidayar kusan dukanin kuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar lahadi, wanda ke nuna cewa fitaccen shugaban ƙasar Laurent Bagbo shi ne ke gaban sanan tsofon framinista Alassane Ouattara na take masa baya.

To sai dai a halin da ake ciki tsofon shugaban ƙasar Henri Konan Bedie ya bukaci da hukumar zaɓen ta sake lisafin ƙuri'un saboda abinda ya kira kurakurai da ya ce sun samun shaidun cewa an tabka a lokacin kada ƙuria'ar.

Alphonse Djedje Mady shi ne shugaban yaƙin neman zabe na tsofon shugaban ƙasar ya kuma ce:

"Jam'iyyarmu ta PdCi na da shakku akan sahihancin sakamakon wannan zaɓe kuma PdCi na yin Allah waddai da yunƙurin jirkita sakamakon."

Yanzu haka dai rahotanin dake zowa mana daga Abidjan shelkwatar kasuwancin ƙasar sun ce wasu ɗaruruwan matasa magoya bayan Henri Konan Bedie sun gudanar da zanga zanga tare da ƙone tayoyi da kuma saka shingaye dake daddatse mayan tituna na birnin tare kuma da yin kira ga shugaban hukumar zaɓen wanda shi ma ɗan jam'iyar ne ta Bedie wato Youssou Bakayogo da ya yi marabus.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane

Edita: Ahmad Tijani Lawal