1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-Zangar ma'aikata a Italiya

June 26, 2010

An dai gudanar da wannan zanga-zanga ne a birane daban-daban da suka haɗa da Roma da Milan.

https://p.dw.com/p/O3oN
Masu Zanga-Zanga a ItaliyaHoto: picture alliance/dpa

Ƙungiyar ƙwadago mafi girma a Italiya ta gudanar da wani gagarumin yajin aikin gama gari da nufin tilastawa gwamnati sauya manufa akan matakan tsuke bakin aljihun gwamnati na Euro biliyan 25.

An dai gudanar da wannan zanga-zanga ne a birane daban-daban da suka haɗa da Roma da Milan.

Yajin aikin dai ya haifar da rarrabuwan kawuna a tsakanin al'uman ƙasar tsakanin wayan da ke ganin yajin aikin ba zai taimaka wajen kawo sauyi ba da kuma masu akasin wannan ra'ayi.

Duk da wannan yajin aikin motocin Safa-Safa da Jiragen ƙarƙashin ƙasa sunci gaba da zirga-zirga.

Yajin aikin na Italiya ya biyo bayan yajin aikin da ma'aika suka gudanar a ƙasashen Faransa da Girka, duk a wannan mako damin nuna adawa da gyaran dokokin Fansho da kuma rage ƙuɗaɗen kasasfin kuɗin bana da gwamnatocin ƙasashen na Turai ke ɗauka domin tsuke bakin aljuhu.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed Abubakar