1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar ma'aikata a Faransa

Ƙungiyoyin ƙwodago sun yi watsi da matakin da gwamnatin Faransa ke son ɗoka na ƙara skekaru biyu daga shekaru 60 na yin ritaya

default

Gwamnatin shugaba Nikola Sarkozy na Faransa, na shirin fuskantar zanga- zanga mafi girma ta ƙungiyoyin ƙwodago da ke shirin bazuwa yau a kan tituna, domin yin watsi da wata doka da ke shirin yin gyaran fuska ga tsarin kundin ma´aikatan ƙasar, mussamman batun ritaya .

Yan ƙwodagon waɗanda su ka ce zasu tattara kamar mutun miliyan biyu a zanga- zangar,

su na adawa ne da dokar da ke yin ƙari ga shekarun yin ritaya a ƙasar, wanda gwamnatin ta ke son ta mayar da shi daga shekaru 60 zuwa 62 kafin nan da shekara ta 2018.

Wannan zanga zanga wacce ita ce ta ukku da za a yi ,ta zo ne a daidai lokacin da Majalisar ɗokoki ta ƙasar ke fara mahawara akan dokar, wanda gwamnatin ke son a amince da ita a cikin watan Oktoba mai zuwa , wanda kuma bisa ga dukan alamu za ta fuskanci ƙalubale na jam'iyyun gurguzu na adawa.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Yahuza Sadissu Madobi