1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar likitoci a Jamus

December 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvIO

Dubban likitoci daga asibitocin koyarwa 20 anan Jamus suka yi wata zanga zanga a yau suna masu barazanar shiga yajin aiki,suna masu bukatar karin albashi da inganta yanayin aikinsu.

Anan birnin Bonn likitocin sun taru a bakin asibitin koyarwa suna dauke da kwalaye da suke dauke da rubuce rubuce da ke nuna gajiyar da suka yi da rashin karin albashinsu.

Hakazalika a garuwan Leipzig,da Koln likitocin sun gudanar da irin wannan zanga zanga .

Wani dalili kuma na wannan zanga zanga shine,akan wani shirin gwamnati na jinkirta aiwatarda dokar da ta kara tsawon lokutan aiki har sai nan da shekara guda kafin ta fara aiki.

Dokar dai wadda tun farko ya kamata ta fara aiki ranar daya ga watan janairu,zata tilastawa masu bada aiki biyan likitoci tsawon lokuta da sukayi aiki.

Kungiyar ta likitoci kuma tana kuma bukatar karin kashi 30 cikin dari na albashin maaikatanta 22,000 da suke aiki a asibitocin koyarwa na Jamus.