1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar likitoci a Jamus

Dubban likitoci da maáikatan jinya da masu harhada magunguna a nan Jamus sun gudanar da zanga zangar gama gari domin nuna adawa da matakan garanbawul da shugabar gwamnati Angela Merkel ke shirin fara aiwatarwa ga harkokin lafiya a nan jamus. An gudanar da zanga zangar a jihohi goma sha daya a fadin tarayyar Jamus domin fadakar da jamaá cikakkiyar manufar gwamnatin na ragin tallafi ga harkokin lafiya. A kusan dukkanin asibitoci an kafa sashen fadakarwa domin wayar da kan marasa lafiya a game da manufar ta gwamnati.