Zanga zangar kin jinin Amurka a Indonesia | Labarai | DW | 05.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar kin jinin Amurka a Indonesia

Dubban musulmi ne sukayi wata zanga zangar lumana a kofar ofishin jakadancin Amurka dake Jakarta ,domin bayyana rashin jin dadinsu dangane da cigaban tashe tashen hankula a Iraki da Afganistan.Kungiyar data shirya gangamin mai suna Hizbut Tahrir,itace keda alhakin gudanar da campaign kafa kasar In donesia tun shekarun 1920.Daga cikin mutane dubu 5 da suka gudanar da wannan gangami da safiyar yau,4rabinsu mata ne.An dai tura kimanin yansanda dubu 2 domin hana masu zanga zangar shiga harabar ofishin jakadancin Amurkan dake Jakarta.Masu gangamin dai suna wake na nuna kin jinin Amurka, tare da kiraga dakarunta dasu fice daga Iraki da Afganistan.Bugu da kari suna kuma dauke da kwalaye dake Allah wadan cigaban gurbata muhalli da Amurka takeyi da kamfaninta dake gunduwar Papua.