1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar Hebollah a Lebanon

Jamian tsaro a kasar Lebanon sun shiga cikin shirin ko ta kwana,yayinda kungiyar Hezbollah da kawayenta masu goyon bayan Syria suka kaddamar da wata babbar zanga zanga a yau jumaa,suna masu kira da rushe gwamnatin kasar dake da goyon bayan Amurka.

Wasu suna ganin cewa wannan zanga zanga zata koma wani taho mu gama ne tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu haka dai jamian tsaron Lebanon sun jibge dakarunsu a bakin ofishin Firaminista Siniora saboda tsoron ko masu zanga zangar zasu nemi kai farmaki .

Kodayake kungiyar ta Hezbollah wadda ta dakatar da zanga zangar tun farko saboda kashe ministan kasar da akayi,tace zata yi zanga zangar ta lumana.

A nashi bangare dai firaminisra Foud Siniora ya sha alwashin kare duk wani abinda zai bata harkokin demokradiya na kasar