1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar goyon bayan gwamnati a Iran

Abdullahi Tanko Bala
January 3, 2018

Dubban jama'a sun gudanar da zanga zangar nuna goyon bayan gwamnatin Iran a birane da dama na kasar, bayan tsawon kwanaki ana tashe tashen hankula.

https://p.dw.com/p/2qI4A
Iran Demonstration für die Regierung
Dubban masu zanga zangar nuna goyon baya ga gwamnati a birnin TehranHoto: Reuters/Tasnim News Agency

Masu zanga zangar wadanda ke dauke da tutar kasar da kuma hoton jagoran addini Ayatollah Ali Khamenei sun yi ta rera kasidu na la'antar wadanda suka kira maciya amanar kasa.

Amirka ta ci gaba da matsin lamba akan kasar ta Jamhuriyar musulunci, inda jakadar Amirkar a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta yi kiran da a gudanar da taron gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da ake ciki a Iran.

A na ta bangaren gwamnatin Jamus, a ta bakin kakakinta Ulrike Demner ta ce ta na sa ido akan abin da ke faruwa na zanga zangar da jama'a ke yi saboda matsin tattalin arziki, ta kuma bukaci hukumomin su martaba bukatun jama'a dama  tattaunawa da masu zanga zangar domin samun masalaha.