Zanga zangar dubai jama′a a Ƙasar Amurka | Labarai | DW | 26.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar dubai jama'a a Ƙasar Amurka

Jerin gwano haɗe da maci a jihar Arizona ta Amurka na jama'a domin yin Allah wadai da wata doka akan baƙin haure

default

Duban jama'a sun gudanar da zanga zanga tare da yin jerin gwano cikin lumana a Phoenix hed kwatar jihar Arizona, da ke a kudu ma so yammacin Amurka, domin yin Allah wadai da wata tsatsaura dokar, kan baƙin haure , da gwamna jihar ta sa hannu akan ta a ranar juma'a da ta gabata. Dokar wace ke baiwa yan sanda damar kama duk wani wanda ake da shaku akansa da ya shigo ƙasar ba kan ƙaida ba, na shan kakausar suka daga yan adawa.

A cikin mutane da suka yi zanga zangar a ƙarshen mako a jihar ta Arizona hada magajin garin New York dakuma wasu wakilai na ƙungiyoyin kare hakin jama'a.

Dokar wace za ta fara aiki nan gaba a cikin watannin ukku masu zuwa, jama'a sun yi barazanar ci gaba da zanga zanga kafin lokacin har sai gwamnatin ta yi watsi da ita.

Yanzu haka dai ana ƙiyasta kamar mutun dubu ɗari fuɗu da sittin dake zaman baƙin haure a jihar ta Arizona waɗanda basu da cikkakun takardu na samun izinin zama a Amurka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Mohamed Nassiru Awal