Zanga zangar adawa da ziyarar paparoma a turkiyya | Labarai | DW | 26.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar adawa da ziyarar paparoma a turkiyya

Dubban masu zanga zanga ne sukayi gangami a birnin Istambul din kasar Turkiyya domin nuna adawa da ziyara da paparoma Benedict na 16 zai kai kasar,wanda zai fara ranar talata.Shuganannin jammiyun siyasa na addinin Islama ne suka shirya wannan boren,adangane da abunda suka danganta da sabawa addinin da kalaman paparoman yayi,a jawabinsda na watan satumban daya gabata,inda ya dangana addinin islama da ayyukan tarzoma.Rangadin Pasparoma a turkiyyan dai,zai kasance ziyara irinsa na farko daya kai kasa dake da musulmi,a matsayin mafi yawan alummarta.