Zanga-Zangar adawa da Siriya a Beirut | Siyasa | DW | 14.03.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-Zangar adawa da Siriya a Beirut

Dubban daruruwan mutane suka hadu a tsakiyar birnin Beirut domin bayyana adawarsu ga kasar Siriya wata daya bayan kisan gillar da aka yi wa tsofon P/M Rafik Hariri

Zanga-zangar adawa da Siriya a Beirut

Zanga-zangar adawa da Siriya a Beirut

Dubban daruruwan mutane dake dauke da tutoci daga sassa dabam-dabam na kasar Lebanon suka hallara a wani dandalin dake kusa da makabartar da aka binne tsofon Piraminista Rafik Hariri domin yin kira da a dauki wani matakin bincike na kasa da kasa akan kisan gillar da aka yi masa da korar shugaban jami’an tsaron kasar dake samun goyan bayan Siriya da kuma janyewar asakarawan Siriyar baki daya daga Lebanon. Bisa sabanin zanga-zangar da aka rika gudanarwa tun bayan harin bom da aka kai kan Hariri a ranar 14 ga watan fabarairu da ya wuce, a wannan karon da yawa daga Musulmi ‘yan Sunna sun ba da hadin kai ga ‘yan Druz da Kiristoci wajen gudanar da zanga-zangar ta adawa da Siriya. Manazarta na ganin cewar wannan zanga-zangar ta zo ne domin mayar da martani akan wata zanga-zangar da ‘yan Shi’a, a karkashin jagorancin kungiyar Hizballah, suka gudanar a kudancin Lebanon a jiya lahadi domin adawa da kasar Amurka. Mai yiwuwa zanga-zangar ta yau ta zama ta karshe daga jerin zanga-zangar da ake ta fuskanta a birnin Beirut tun bayan kisan gillar da aka yi wa tsofon piraminista Rafik Hariri, domin neman janyewar sojojin Siriya daga kasar Lebanon. Wasu majiyoyi na siyasa sun ce akwai fargabar fuskantar tashe-tashen hankula sakamakon sabanin siyasar dake akwai tsakanin bangarorin kasar dabam-dabam a game da rawar da Siriya ke takawa tun bayan mutuwar Hariri, duk da cewar kawo yanzu zanga-zangar na tafiya a cikin lumana. A yanzu haka mahukunta sun fara duba yiwuwar amfani da sojoji domin haramta ci gaban zanga-zangar. Shugaba Emile Lahoud da sauran masu goyan bayan Siriya sun yi kira game da dakatar da zanga-zangar da kuma shiga shawarwarin neman bakin zaren warware rikicin siyasar Lebanon. A makon da ya gabata dubban daruruwan mutane suka hadu a tsakiyar birnin Beirut domin nuna goyan bayansu game da yi wa dakarun kungiyar Hizballah damarar makamai da kuma gode wa kasar Siriya a game da tura sojojinta da tayi domin shisshigi a yakin basasar Lebanon a shekara 1976. Rahotanni sun ce tuni Siriya ta janye sojoji dubu 4 daga cikin sojoji dubu 14 da ta tsugunar a Lebanon, kuma a cikin kwanaki uku masu zuwa za a gama kwashe wasu sojojin a mataki na biyu na janyewarta daga Lebanon.