Zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓe a Togo | Labarai | DW | 09.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓe a Togo

Jami'an tsaro a Togo sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa gangamin adawa da zaɓe

default

'Yan san sandan kwantar da tarzoma na ƙasar Togo sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a makon da ya gabata. Gungun matasa da yawansu ya kai 400 ne suka fantsama akan titunan Lome babban birnin ƙasar domin yin Allah wadai da aringizon ƙuri´u da kuma murɗiya da ya bai wa Faure Gnasingbe damar yin tazarce. Sai dai gwamanti ta nunar da cewa zanga-zangar ta saɓa ma doka. Babbar jam´iyar adawa ta ƙasar ta Togo wato UFC da kuma wasu ƙarin jam´iyu uku ne suka kira wannan ganganmin domin nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen. Hukumar zaɓen ƙasar ta Togo ta nunar da cewa shugaba Gnasingbe mai barin gado ya lashe kashi 60 daga cikin 100 na ƙuri´un da aka kaɗa, yayin da sabon madugun 'yan adawa wato Jean Pierre Fabre ya tashi da kashi 33 daga cikin 100.

Mawallafi:Mouhammadou Awal Edita: Zainab Mohammed