Zanga-Zangar Adawa Da Manufofin Gwamnati | Siyasa | DW | 30.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-Zangar Adawa Da Manufofin Gwamnati

Tun misalin makonni biyar da suka wuce dubban mutane ke gudanar da zanga-zanga a kowace ranar litinin domin bayyana adawarsu da manufofin garambawul da gwamnatin Gerhard Schröder ke da niyyar gabatarwa tun daga watan janairu na badi idan Allah Ya kaimu

Masu zanga-zanga a kowace litinin a birnin Leipzig

Masu zanga-zanga a kowace litinin a birnin Leipzig

Yau dai kimanin makonni biyar ke nan a jere da aka gabatar da matakin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati a kowace ranar litinin. Amma fa mutane a kasashen dake makobtaka da Jamus sai mamaki suke yi a game da wannan adawa, wacce ta shafi wasu matakai na garambawul, wadanda ba makawa game da su. ‚Yan jarida daga kasashen ketare sun hakikance cewar babu wata kasa ta nahiyar Turai dake kula da makomar jin dadin rayuwar Jama’ara kamar Jamus. A lokacin da yake bayani game da haka Betrand Benoit, mai aike wa da jaridar Financial Times rahotanni daga Berlin cewa yayi:

Tsarin jin-dadin rayuwar jama’a a Jamus ya fi na kowace kasa ta nahiyar Turai nagarta. Amma a yanzu kasar zata shiga rukunin sauran kasashen Turai wajen hana cin gajiyar tallafi na gwamnati ga marasa aikin yi, har sai illa-masha-Allahu, kamar yadda lamarin yake a zamanin baya.

A da can dai al’umar kasar su kan dogara ne kacokam akan gwamnati, musamman ma a gabacin Jamus sakamakon wanzuwa a karkashin mulkin ‚yan kwaminis. Ainifin musabbabin ta da kayar baya da masu zanga-zangar ke yi shi ne sabo da suka yi da dogaro akan irin wannan tallafi, inda mutum zai yi tsawon shekaru da dama yana samun taimako daga gwamnati bayan yayi asarar aikinsa. Kokari da gwamnati ke yi na dakatar da wannan manufa ya sanya wasu na ganin tamkar wani yunkuri ne na tauye hakkinsu. Amma fa daukar wannan mataki wajibi ne ta la’akari da mawuyacin halin da tattalin arzikin Jamus ke ciki a cewar Pierre Bocef, mai aikewa da jaridar Le Figaro ta kasar Faransa rahotanni daga Berlin. Ya ce a halin yanzu haka jami’an siyasar Faransa sun sa ido suna kallon fadi-tashin da ake fuskanta a Jamus, suna kuma ya ba wa shugaban gwamnati Gerhard Schröder a game da kurarinsa na aiwatar da garambawul. Ainifin wannan abin dake faruwa a nan Jamus, an fuskanci shigensa a kasar Sweden a cikin shekarun 1990, inda gwamnati ta gabatar da tsauraran matakai na tsumulmular yawan abin da take kashewa a fannin jin dadin rayuwar jama'a kuma ta haka aka samu kafar kare makomar tsarin kyautata zamantakewar jama’a a wannan kasa. A wancan lokaci shirin na gwamnati ya samu cikakken goyan baya daga al’uma. Babban kuskure da Jamus tayi shi ne kin gabatar da wannan mataki tun a shekarun na 1990 daidai da sauran kawayenta na nahiyar Turai. Matakan na garambawul ba zasu yi nasara ba sai tare da goyan bayan jama’a da kuma dagewa daga bangaren gwamnati, dake cikin hali na kaka-nika-yi yanzu haka. A bangare guda ana fama da zanga-zangar adawa daga jama’a, sannan a daya bangaren kuma Jamus na bukatar bunkasar tattalin arziki domin tinkarar matsalar marasa aikin yi wadanda yawansu ke dada karuwa.