Adawa da manufar kodago ta shugaba Macron
September 12, 2017Talla
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jawo kakkausar martani bayan da ya kira masu adawa da manufarsa ta garanbawul ga fannin kodago malalata, kalmar da ta tunzura dubban jama'a fitowa kan tituna domin nuna fushinsu.
Yan siyasa da ke adawa da shugaban ciki har da Marine Le Pen sun yi amfani da wannan dama wajen mayar masa da martani da cewa baya kaunar Faransawa.
Macron mai shekaru 39 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Mayu, farin jininsa na kara faduwa kasa wanwar inda masu sharhi ke danganta lamarin da dagawa da kuma kurakurai ta fuskar siyasa.