1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da Kungiyar PKK a Turkiyya

Mohammad Nasiru Awal | Gazali Abdou Tasawa
December 12, 2016

Mutane da dama suka yi jerin gwano kusa da cibiyar 'yan sandan birnin Santambul a kasar Turkiyya suna masu yin tir da tagwayen hare-haren bam da aka kai kusa da wani filin wasan kwallon kafa na Istanbul.

https://p.dw.com/p/2UADN
Türkei Istanbul nach den Anschlägen
Hoto: Reuters/H. Aldemir

Mutane da dama suka yi jerin gwano kusa da shelkwatar 'yan sandan birnin Santambul a kasar Turkiyya suna masu yin tir da tagwayen hare-haren bam da aka kai kusa da wani filin wasan kwallon kafa da akalla mutane 44 daukacinsu 'yan sanda suka rasu. Wannan macin ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman makoki a fadin kasar ta Turkiyya bayan hare-haren na yammacin ranar Asabar wadanda wata kungiya da ta balle daga kungiyar Kurdawa ta PKK ta dauki alhakin kaiwa. 

 

Kungiyar ma'aikatan gwanati ta shirya wannan maci na yin tir da kungiyar Kurdawa ta PKK da aka haramta ayyukanta a Turkiyya wadda kuma ake zarginta da alaka da Kungiyar Kurdistan Freedom Falcons da ta yi ikirarin kai hare-haren da suka yi sanadiyyar rayuka akalla 44 daukacinsu 'yan sanda. Gulay Firat memba ce ta kungiyar ma'aikatan da ita ma ta shiga cikin zanga-zangar, ta yi kira da a kame masu hannu a wannan ta'asa a hukunta su.

 "Zuciyarmu ta kadu. Dukkanmu iyaye ne muna da 'ya'ya. Wadanda suka yi mutuwar shahadar duk 'ya'yanmu. Ina son a kawo karshen wannan ta'adda domin akwai jini da yawa a kan tutar 'yan PKK. Muna bayan kasarmu da al'ummarmu da kuma jami'an 'yan sandarmu. Ba wanda ya isa ya raba kan wannan kasa."

Türkei Reaktionen nach dem Anschlag in Istanbul - Demonstration
Hoto: picture alliance/NurPhoto/E. Oprukcu

Shi ma shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan da a safiyar wannan Litinin ya halarcin jana'izar da aka yi wa daya daga cikin 'yan sandan da suka rasa ransu ya ce kasar za ta dau fansa kan duk mai hannu cikin wannan ta'asa.

 "Ya kamata sun san cewa ba za su iya tserewa ba. Ba za mu kyale su rika cin karensu babu babbaka ba. Za su dandani kudarsu. Su san da wannan."

Tun lokacin da Turkiyya ta fara daukar matakan soji a kan Kurdawa da ke Kudu maso Gabashin kasar, masu matsanancin ra'ayi a cikin Kurdawan ke yi ta kai munanan hare-haren cikin Turkiyya, lamarin da ke harzuka akasarin 'yan kasar, kamar dai wannan mutumin da ke zaune kusa da wurin da aka kai harin na wannan Asabar.

 "Kanmu a hade yake. Tun kimanin shekarun 30 da suka wuce wasu abubuwa ke faruwa a wannan kasa. Kantomomi da Firaministoci da shugabannin kasarmu ba sa gudanar da aikinsu daidai. Idan za su yi aikinsu da kyau ba za mu samu wariya ba ko takaddama tsakanin jam'iyyun siyasa."

Türkei Istanbul nach den Anschlägen
Hoto: Reuters/M. Sezer

Kasashen duniya na ci gaba da aike sakonnin jaje ga kasar ta Turkiyya. A lokacin da yake magana a birnin Brussels yayin taron ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai kan dangantaka da Afirka ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Marc Ayrault cewa ya yi.


"Ina jaje dangane da munanan hare-hare da aka kai Turkiyya a karshen mako. Ina nuna kudurinmu na yaki da ta'addanci na kungiyoyi irinsu IS da PKK da sauran nau'o'in ayyukan tarzoma."

A halin da ake ciki ofishin Firaministan Turkiyya ya sanya takunkumi kan watsa hotuna ko faya-fayen harin, da za su iya haddasa tsoro cikin jama'a, wanda dama shi ne burin 'yan ta'addar.