Zanga-zangar adawa da gwamnatin Moroko | Labarai | DW | 29.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar adawa da gwamnatin Moroko

Dubban mutane suka yi zanga-zanga domin ganin an dauki mataki kan yaki da cin hanci da kuma kyautata aikin malaman makarantu.

Dubban 'yan kasar Moroko ne suka yi zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suke neman sai a dau matakan yaki da cin hanci, kana a kyautata aikin malaman makarantu. Kimanin kungiyoyin kwadago 1000 suka kira magoya bayansu domin shiga zanga-zangar da aka yi Rabat babban birnin kasar ta Moroko.

Bayaga kungiyoyi kwadago, wasu 'yan jam'iyyun adawa da masu fafitikar kare hakkin jama'a sun shiga zanga-zangar. Daga bisani wasu malaman makaranta kimanin 2000 suka yi dafifi a gaban majalisar dokoki, inda suke cewa dole a soke ayar doka wace ta rage almabashinsu.