Zanga zangar adawa a yankin palasdinawa | Labarai | DW | 16.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar adawa a yankin palasdinawa

Dubban magoya bayan gwamnatin Hamas ,dauke da makamai nesukayi gangami da yammacin yau a zirin gaza,domin bayyana adawansu da kiran da shugaban yankin na Palasdinawa Mahmoud Abbas yayi na a gudanar da zabe cikin gaggawa,batu kuma da Hamas mai mulki tace ka iya jefa yankin a yakin basasa.Daruruwan magoya bayan hamas din rurrufe da fuska da bakaken kyallaye dauke da makamai suka kai somame harabar majalisar dokoki dake Gaza,bayan kiran da akayi na gudanar da wannan gangami.Ministan harkokin waje na gwamnatin Hamas Mahmud al-Zahar ya bayyana adawansu da wannan yunkuri na shugaban palasdinawa Abu Mazin.