Zanga zangar adawa a Venezuela | Labarai | DW | 29.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar adawa a Venezuela

Dubban masu zanga zanga a ƙasar Venezuela sun yi arangama da yan sanda, inda jamián tsaron suka buɗe musu wuta da harsasan roba da kuma barkonon tsohuwa. Masu zanga zangar waɗanda suka yi gangami a birnin Caracas na adawa ne da matakin da gwamnatin ta ɗauka na rufe wani gidan talabijin mai zaman kan sa. Tun dai bayan da shugaban ƙasar Hugo Chavez ya bada umarnin rufe gidan Radiyon da kuma Talabijin mai zaman kan sa dake birnin Caracas a ranar lahadin da ta wuce, jamaá suke ta zanga zanga a kusan dukkan manyan birane a ƙasar ta kudancin Amurka inda suke sukar gwamnatin da danne yan adawa. Matakin dai ya haifar da yin Allah wadai daga sassan ƙasashen duniya abin da suka ce yiwa dimokraɗiya karan tsaye ne.