1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar adawa a Thailand

April 25, 2010

Firaministan Thailand yace ba zai bada kai bori ya hau ba ga masu zanga zangar adawa.

https://p.dw.com/p/N5yi
Fira´ministan Thailand Abhisit Vejjajiva.Hoto: picture alliance / dpa

Firaministan Thailand Abhisit Veijajiva yace ba zai bada kai bori ya hau ba ga masu zanga zangar adawa da gwamnati. Firaministan ya yi wannan furucin ne a jawabin da ya yiwa al'umar kasar ta akwatunan Talabijin bayan da ya yi fatali da tayin masalahar da masu zanga zangar adawar suka gabatar ta neman a gudanar da sabon zaɓe. Masu zanga zangar dai magoya bayan tsohon Firaministan kasar ne Thaksin Shinawatra, suna kuma buƙatar Firaministan ya rusa majalisar dokoki tare da kiran sabon zaɓe cikin kwanaki 90. Tarzomar da ta auku ta a baya ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 26 yayin da wasu mutanen kusan 1,000 kuma suka sami raunuka tun bayan da masu zanga zangar waɗanda ke sanye da jajayen riguna suka fara mamaye muhimman wurare da suka haɗa dana yawon buɗe idanu da kuma manyan kantuna a tsakiyar birnin Bangkok fiye da kwanaki 30 da suka wuce.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

  Edita   : Mohammed Nasir Awal