Zanga zangar adawa a Thailand | Labarai | DW | 14.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar adawa a Thailand

Masu zanga zanga a Thailand sun buƙaci gudanar da sabon Zaɓe

default

Dubban masu zanga zangar adawa da gwamnatin Thailand a iBangkok

Aƙalla mutane kimamin 80,000 ne magoya bayan tsahon Firimiyan ƙasar Thailand Thaksin Shinawatra suka yi gangami a Bangkok yawancinsu daga yankunan karkara, inda suke kiran gudanar da sabon zaɓe.

A jawabin da yayi ta akwatin Talabijin, Firaministan ƙasar Abhisit Vejjajiva wanda yake da sauran waádin mulki har zuwa ƙarshen shekarar baɗi yace ko kusa gwamnati ba zata amince da buƙatar yin zaɓen gabanin waádi ba.

Masu zanga zangar waɗanda ke sanye da jajayen riguna, kuma magoya bayan tsohon Firaminista Thaksin Shinawatra wanda aka hambarar da gwamnatinsa a wani juyin mulki a shekarar 2006 sun yi barazanar yin tattaki zuwa barikokin soji a wajen Bangkok inda sojojin ke gadin Firaminista Abhisit Vejjajiva da sauran ministocin gwamnati.

Thaksin Shinawatra

Tsohon Firaministan Thailand Thaksin Shinawatra

A yau lahadi hukumomin Thailand sun baza jamián tsaro 50,000 a faɗin Bangkok babban birnin ƙasar domin tabbatar da doka da oda.

A wani sakon Video da ya aike daga wani wuri da baá baiyana ba, amma ake zato a nahiyar turai ne Thaksin ya buƙaci magoya bayansa su tashi haikan domin ƙwato yancinsu.

Makonni biyu da suka wuce kotun ƙolin Thailand ta kwace Dala miliyan dubu da ɗari huɗu daga cikin kadarorin da ya mallaka.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Ahmed Tijani Lawal