1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar Adawa a kasar Spain

March 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuPv

Dubban yan kasar Spain sun gudanar da zanga zangar adawa a birnin Madrid domin nuna rashin jin dadi da matakin da gwamnati ke dauka na yin sassauci ga kungiyar yan aware ta ETA. Masu zanga zangar sun fusata ta shawarar da gwamnati ta yanke na sassaucin matakai a kan wani fursuna dan ETA wanda ya sami rashin lafiya sakamakon yajin cin abinci. Masu zanga zangar sun bukaci P/M Jose Luis Zepatero da ya yi murabus. Babbar jamíyar adawa ta Spain wadda ta jagoranci zanga zangar ta zargi gwamnati da mika wuya ga kungiyar ETA. A shekarar da ta gabata, gwamnati ta janye shirin sulhu da kungiyar awaren ta ETA saboda wani hari da ta kai a filin jirgin saman Madrid a watan Disamba.