Zanga zangar adawa a Belarus ya sami ƙarin tagomashi | Labarai | DW | 22.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar adawa a Belarus ya sami ƙarin tagomashi

A ƙasar Belarus jakadu da dama na ƙasashen turai, sun bi sahun masu zanga zangar adawa da sakamakon zaɓen da ya baiwa shugaban kama karya Alexander Lukashenko nasar sake yin tazarce. Masu zanga zangar sun shafe kwanaki biyu suna zaman darsham a dandalin Oktyabrskaya a garin Minsk. Babban madugun adawar Alexander Milinkevich ya yi kiran gudanar da gagarumar zanga zanga ta ƙin amincewa da sakamakon zaɓen. Masu zanga zangar na buƙatar sake gudanar da zaɓen sannan a haramtawa shugaban ƙasar Lukashenko wanda ya shafe shekaru goma sha biyu yana mukin ƙasar tsayawa takara. ƙasashen yammacin turai sun Allah wadai da zaɓen na ranar Lahadi wanda suka ce bai cimma kaídojin zaɓe na kasa da kasa ba.