Zanga zangar Adawa a ƙasar Zambia | Labarai | DW | 02.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar Adawa a ƙasar Zambia

Shugaban ƙasar Zambia Levy Mwanasa ya buƙaci samun zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan da gungun magoya bayan yan adawa suka gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da sakamakon farko na zaɓen da aka gudanar a ƙasar a ranar alhamis ɗin da ta gabata, wanda ke nuni da cewa Mwanasa ya kama hanyar lashe zaɓen. Magoya bayan jamíyar Patriotic Front ta madugun adawa Michael Sata sun bazama yankunan birnin Lusaka suna farfasa motoci tare da jifar yan sanda da duwatsu suna ikrarin ba za su amince da sakamakon zaɓen ba. Badakalar ta ɓarke ne bayan da aka baiyana sakamakon farko na zaɓen wanda ya nuna madugun adawar Michael Sata wanda da farko yake kan gaba ya komo mataki na uku bayan ƙidayar ƙuriú fiye da kashi 80 na lardunan ƙasar. Sata ya jaddada cewa imanin cewa shi ya lashe zaɓen, ya kuma yi kakkausar suka ga hukumar zaɓen wadda yace ta rike sakamakon mazaɓu inda yake da rinjaye.