Zanga zangar a kudancin Nigeria | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zangar a kudancin Nigeria

Jami´an tsaro a tarraya Nigeria sun harbe har lahira wasu matasa 2, sun kuma jikata wasu karin murtane 3, a kwana na farko, na zangar zangar da kungiyar Massob ta shirya a Onitsa, dake kudancin kasar.

Kakakin kungiyar Massob ,mai neman kaffa kasa mai cikkakenn yanci ta Biafra a kudancin Nigeria, ya sanar maneman labarai cewa, jami´an tsaro sunyi ta harbin kan mai uwa da wabi, wanda a sakamakon hakan ya jawo assara rayuka, saidai duk za su ci gaba da gwagwarma har sai sun cimma sun cimma burin su.

A nasa bangare wani jagoran yan sandar Awada, ya karyata wannan batu da cewar babu mutumen da ya rasa rai a cikin wannan zanga zanga.

Kungiyar Massob, ta gayyaci daukacin al´ummomin yankin Biafra, da su kauracewa wauraren ayyukan su, yau litinin da gobe, talata,rahotani kuma sun tabatar da kiran nasu, ya samu karbuwa a biranen Onitsa Oweri da Akwa, inda komi ya tsaya cik , a yau litinin.