Zanga zanga na ci gaba da bazuwa a garuruwan kewayen birnin Paris | Labarai | DW | 03.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga na ci gaba da bazuwa a garuruwan kewayen birnin Paris

Kwanaki 7 jerai jerai a kasar Fransa mazamna garuruwan da ke kewayen Paris babban birnin Kasar ke shirya zanga zanga.

A daren jiya garuruwa 9 ne, su ka tada kayar baya a da´irar Seine Saint denis, inda su a kona motoci fiye da 40.

Wanan riginginmu su fara tun satin da ya wuce a garin Kilishi Sous Bois bayan mutuwar wasu matasa guda 2.

A yammacin jiya majalisar dokoki ta saurari praminista Dominique de Villepin, da kuma Ministan cikin gida Nikola Sarkozy a game da wannan tashe tashen hankulla.

Yan majalisar adawa sun zargi ministan cikin gida da rura wutar rikicin, ta hanyar gayin bakaken manganganu, ga masu zanga zangar

Kakakin gwamnatin kasar Fransa, ya bayana wa manema labarai matakai daban daban da gwamnati ta dauka, domin maido da kwanciyar hankali a wannan garuruwa.

Ministan cikin gida ya je daren jiya, wuraren da arangamar ke gudana, inda ya kiri taro gaggawa tare da wakilai daban daban na al´ummomi, da kuma jami´an tsaro.