1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga kan yan gudun hijirar Zimbabwe

December 11, 2007
https://p.dw.com/p/Ca0M

A ƙasar Afrika ta kudu masu zanga zanga sun ƙona wasu gidaje 60 na jeka na yi ka na yan gudun hijirar Zimbabwe. Mazauna yankin da sansanin Mooiplaas yake da sukayi zanga zangar a daren jiya sun zargi yan gudun hijira ta Zimbabwe da aikata muggan laifuka a yankin. An ƙiyasta cewa yawan yan kasar Zimbabwe da sukayi gudun hijira zuwa Afrika ta Kudu sun kai aƙalla mutane miliyan biyu zuwa miliyan biyu da rabi,bayan zargin shugaba Robert Mugabe da laifin take hakkin bil adama.