1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga kan dagwalon nukiliya

November 8, 2010

An gudanar da zanga-zangar adawa da jibge dwagwalon nukiliya a garin Gorleben da ke Jamus.

https://p.dw.com/p/Q1IS
'Yan zanga-zangar adawa da dagwalon nukiliya zazzaune akan layin dogo.Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan sanda a nan Jamus na ci gaba da ƙoƙarin kawar da shingayen da ɗaruruwan masu zanga-zangar adawa da dagwalon sharar nukiliya suka gindaya akan layin dogo domin hana jigilar dagwalon nukiliyar da yawansa ya kai ton 120 zuwa cibiyar ajiyar da ke garin Gorleben. Wani mai magana da yawun 'yan sandan ya baiyana aikin kawar da shigayen daga layin dogon da cewa aiki ne mawuyaci amma yana tafiya cikin kwanciyar hankali. Ya ce wasu daga cikin masu zanga-zangar sun bar wurin don radin kansu yayin da wasu sai da aka yi amfani da ƙarfi domin janye su. Masu zanga-zangar waɗanda suka haɗa da 'yan siyasa na jam'iyar Green mai rajin kare muhalli sun zargi 'yan sanda da yin amfani da ƙarfin tsiya yayin da suke ƙoƙarin kawar da shingayen ga jiragen ƙasar da suka ɗauko dagwalon sharar nukiliyar. Cibiyar sarrafa dagwalon nukiliyar da ke Gorleben ta yi ƙaurin suna musamman bayan da gwamnati ta sanar da aniyar tsawaita amfani da tashoshin makamashin nukiliyar da ke nan Jamus, matakin kuma da ya fuskanci kakkausar suka daga al'umar ƙasa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala

Edita: Halima Balaraba Abbas