Zanga-zanga game da gurɓattatar shara | Labarai | DW | 06.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga game da gurɓattatar shara

Ƙungiyoyin kare mahalli a Faransa da Jamus sun tada tarzoma don nuna adawa ga jirgin Castor mai jigilar shara mai guba

default

Jirgin jigilar shara mai guba

Ƙungiyoyin kare mahalli sun shirya zanga-zanga a ƙasashen Faransa da Jamus, domin nuna adawa da jigilar gurɓattatar shara mai guba da wani jirgin ƙasa ya ɗauko daga Faransa zuwa Jamus. A halin da ake ciki jirgin ya canza hanya, domin kaucewa masu zanga-zangar.

Hukumomin ƙasashen biyu sun jera 'yan sanda 1600 a tsawan kilomita 1000 da jirgin zai share.

Za a zubar da wannan shara mai nauyin ton 123 kusa da wani birni mai suna Gorleben da ke arewancin Jamus. Kamfanin Areva da ya tara wannan shara, ya ce an ƙunshe ta a cikin tankuna ta yadda ba za ta zama illa ba, ga yanayi ko kuma ga rayuwar ɗan Adam.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal