Zanga zanga a Thailand | Labarai | DW | 16.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Thailand

A kasar Thailand magoya bayan hambarren firimiya Thaksin Shinawatra sun sha alwashin gudanar da wani babban gangami a yau asabar suna msu adawa da gwamnatin mulkin soja data hambarar da shi.

Wadanda suka shirya wannan zanga zanga sunce akalla mutane 50,000 ne ake sa ran zasu hallara wani dandali a tsakiyar birnin Bangkok inda masu zanga zanga suke taruwa a kullum makonni byiu da suka shige suna bukatar kawo karshen mulkin soja a kasar.

Zanga zanagr ta yau tazo ne bayan wani jawabi da Thaksin yayiwa dubban maogaya bayansa ta hanyar bidiyo,yana mai kira ga shugabanin sojin da su tabbatar da an gudanar da zabe a watan disamba kamar yadda suka alkawarta.

Ya kuma yi kira da sasanta tsakani bayan watanni na rikicin siyasa a kasar.