Zanga zanga a Somalia | Labarai | DW | 25.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Somalia

Mayakan gamayyar kotunan Islama sun bude wuta wa masu zanga zanga a garin Kismayo dake kudancin Somaliya.Harbe harben bindigan dai yazo ne adaidai dubban yan somaliyan sukayi jerin gwano akan tituna ,suna rera wakokin nuna adawa da kungiyoyin kotunan musulmin,tare da kone konen tayoyi da jifa da duwatsu ,adangane da cafke garin da kungiyoyin sukayi a daren jiya.Cafke garin Kismayo da kungiyoyin musulmin sukayi ajiyan dai,na nuni da karin madafan ikon kungiyoyin a kudanci da tsakiyar ,wannan kasa tun bayamn karbe birnin Mogadisho daga shugabannin hauloli da Amurka ke marawa baya.Kotunan musulmin dai na tilasta dokokin sharia a dukkan garuruwa dake karkashin madafan ikonsu.A yanzu haka dai gwamnatin rikon kwarya a somalian nada matsuguninta ne a garin Baidoa.

 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5H
 • Kwanan wata 25.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5H