Zanga-zanga a Nijeriya | Labarai | DW | 10.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Nijeriya

Jerin gwanon masu zanga zanga a Abuja.

default

Zanga Zangar lumana kan taƙaddamar shugabanci a Nijeriya.

Kimanin mutane dubu biyar da suka gudanar da jerin gwano a Abujan Nijeriya, sun bukaci a rusa Majalisar Ministocin Nijeriya . Hakazalika sun yi kira ga Shugaba 'Yar'adua da ya fito bainar jama'a makonni biyu bayan dawowarsa daga jinya a kasar Saudiyya. Jami'an 'Yan Sanda sun dakatar da masu zanga - zangar akusa da fadar shugaban ƙasar, inda suka shirya mika bukatunsu ga muƙaddashin shugaban ƙasar, Dakta Goodluck Jonathan. Sakataren gwamnatin tarayyar Nijeriya, Alhaji Mahmud Yayale Ahmad, wanda ya amshi buƙatun masu jerin gwanon a madadin muƙaddashin shugaban ƙasar, ya shaida musu cewar, mukaddashin shugaban ƙasar zai dubi buƙatun nasu ba tare da wani jinkiri ba.

Tunda farko dai, Jagorar masu zanga zangar, Pastor Tunde Bakare, ya bayyana cewar, zasu ci gaba da neman goyon bayan 'yan Nijeriya har sai sun sami biyan bukatar rusa majalisar ministocin ƙasar, da kuma bayyanar shugaban a fili. A ɗaya hannun kuma wasu magoya bayan shugaban Nijeriyar, suma sun yi nasu jerin gwanon, inda suka ce, shugaba 'Yar'adua ne zasu ci gaba da baiwa goyon baya ko ana Ha maza, Ha mata.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Abdullahi Tanko Bala