Zanga zanga a Nairobi | Labarai | DW | 07.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a Nairobi

A birnin Nairobi na ƙasar Kenya, dubunan mutane, sun shirya zanga zanga a sahiyar yau, domin yin tur da Allah wadai, ga harin da wasu yan sandan gwamnati ,su ka kaiwa, wata kafar sadarwa mai zaman kanta, a makon da ya gabata.

Madugun yan adawar ƙasar Kenya, Raila Odinga da ya kiri wannan zanga zanga, ya bayyana halin ni yasu, da yan jarida su ka sami kan su ciki, a wannan ƙasa.

Masu zanga zangar, sun yi ta nuna, kwalaye, masu kiran shugaban ƙasa Maw Kibaki yayi, murabus daga muƙamin sa.

A baya bayan nan, an binciko sama da faɗi da dukiyar jama´a mai tarin yawa,a wannan ƙasa, a sakamakon hakan, wasu daga ministocin da ake zargi da hannu a cikin wannan handama, sunyi murabus.

Ga kuma ,bugu da ƙari, kayin da shugaban ƙasar ya sha, a lokacin da jama´a ta yi watsi da kwaskwarimar da ya buƙaci a shirya ga kundin tsarin mulki.