Zanga-zanga a Myanmar ta ɗauki saban sallo | Labarai | DW | 28.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Myanmar ta ɗauki saban sallo

Rahottani daga ƙasar Maynmar ko kuma Barma, na nunar da cewar dubunan mutane na ci gaba da kwarara a titinan Rangoun babban birnin ƙasar, domin ci gaba da zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati.

Saidai a halin da ake ciki, gwamnati ta jibge yan sanda da sojoji ɗauke da makamai, wanda su ka samu umurnin kawo ƙarshen wannan zanga-zanaga ta ko wane hali.

Wanda su ka ganewa idon su halin da ake ciki, sun nunar da cewar, harakokin kasuwancin su tsaya cik, sannan opishoshi sun rufe kofofin su.

Tsakanin jiya da shekaran jiya, a ƙalla mutane 13 su ka rasa rayuka, a cikin arangama da jami´an tsaro, sannan da dama su ka ji mumunan rauka.

Ƙasashe daban-daban na dunia na ci gaba da yin Allah wadai ga gwamnatin sojojin ƙasar Myanmar, a game da wannan mumunan mataki da ta ɗauka, a kan masu zanga-zangar.

Ranar asabar idan Allah ya kai mu, wakilin musamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, Ibrahim Gambari, zai sauka a birnin Rangoun, domin tantanawa da gwamnatin ƙasar, da zumar kawo ƙarshen wannan tashe-tashen hankula.