Zanga-zanga a Kwango | Labarai | DW | 19.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zanga a Kwango

Daruruwan al'umma a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango sun fantsama kan titunan babban birnin kasar Kishasa don nuna rashin amincewarsu da cigaba da kasancewar da Shugaba Joseph Kabila ke yi kan gadon mulki.

Masu zanga-zangar dai na dauke ne da jajayen kwalaye da ke rubuce da kalamai na kin jinin kasancewar Kabila kan gadon mulki. Jami'an tsaro na kasar dai sun killace muhimman wurare ciki kuwa har da jami'ar Kinshasa inda suka hana jama'a da ke zanga-zanga kaiwa gareta kana sun kara jaddada haramci da aka sanya kan zanga-zanga a kasar.

Rahotanni dai yanzu na cewar shaguna a Kinshasa da sauran sassan kasar sun kasance a rufe, inda a share guda wasu mayakan sa kai suka afkawa wani gidan yari da ke Butembi da ke gabashin kasar wanda hakan ya haifar da tashin hankalin da ya yi sanadin hallakar mutane 6.

Kasashen duniya na cigaba da kira ga 'yan siyasar kasar da Shugaba Kabila kan su yi amfani da hanyoyi na laluma wajen shawo kan wannan dabarwa ta siyasa inda a gefe guda masu rajin kare hakin jama'a ke kira ga Kabila da ya sauka daga mulki maimakon yin tazarce.