Zanga-zanga a kasashen musulmi
February 7, 2006A kasashe daban daban na musulmi a na ci gaba da zanga zangar nuna bacin rai , bayan tozarci da wata jaridar Danmerk ta yi wa Manzan Rahama,ta hanyar zana hotuna, masu suppanta shi da,dan ta´ada.
A Iran bayan zanga zamngar jiya a yau ma dubunan jama´a ne su ka yi cincinrido, a opishin jikadancin Danmark, dake birnin Teheran, saidai Jami´an tsaro su hanna su, kone wannan opishi.
Idan ba a manta ba, kasar Iran, ta bayyana katse duk wasu huldodin cinikayya da Danmerk, domin nuna fushi ga wannan aika aika, da jaridar ta yi.
Kazalika, a birane da dama na kasar Indonisia, masu zanga zangar, sun ci gaba da kone tutocin Danmark.
Hukumomin wannan kasa , sun yi kira ga al´ ummomin su, da ke zaune a Indonesia, Iran Labanon, da Syria da su
Gaggauta fita daga wannan kasashe.