1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zanga a kasar Nepal

April 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2W

Dubban jamaá dake zanga zangar adawa da sarkin Nepal, Gyanendra sun yi arangama da yan sanda a Kathmandu babban birnin kasar. Duk da dokar hana zurga zurgar jamaá da gwamnatin ta sanya, mutane fiye da dubban jamaár sun bujirewa dokar inda suka fita titunan kudancin Nepal da kuma kudu maso yammacin Katmandu inda suke baiyana bacin rai da harbin daya daga cikin masu zanga zangar da jamián tsaro suka yi . An dai tsaurara matakan tsaro inda sojoji da yan sanda ke cigaba da sintiri a manyan titunan kasar. Wani babban jamiín hukumar kare hakkin bil Adama ta majalisar dinkin duniya Ian Martins ya baiyana damuwa da yin amfani da karfin soji a kann masu zanga zanga, yana mai jan hankali da cewa wajibi ne jamián tsaro su yi taka tsantsan domin kare hakkin yan Adam. Kungiyoyin fafutukar cigaban dimokradiyya tare da yan tawayen Maoist sun fara yajin aikin gama gari na kwanaki hudu domin adawa da kwatar mulki da basaraken kasar ya yi a shekarar da ta gabata.