Zanga zanga a kasar Lebanon | Labarai | DW | 23.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga zanga a kasar Lebanon

A kasar Lebanon an rufe hanyoyi da makarantu da kantuna yayyinda dubban jamaa suka fito suna msu amsa kirar ga babbar zanga zanga da kungiyar Hezbollah ta kira a gudanar .

Masu zanga zangar sun kona tayoyi tare da toshe manyan hanyoyi da tituna na cikin birnin Beirut da wasu sassa na kasar.

Wannan zanga zanga itace ta baya bayan nan da yan adawa suka kira a kokarinsu na hambarar da gwamnatin Lebanon mai goyon bayan kasashen yamma,tare neman a gudanar da zabe cikin gaugawa.

Rahotanni sunce firaminista Fouad Siniora yana nan fake cikin ofishinsa dake harabar gidansa,ya kuma shirya bulaguro zuwa Paris domin halartar wata tattaunawa kan halinda ake ciki a Lebanon wanda kasashe masu bada gudumowa suka shirya gudanarwa a ranar alhamis.